Isa ga babban shafi
Nijar

An Rantsar da sabon Shugaban Janhuriyar Nijar Issoufou

A Janhuriyar Nijar a yau Alhamis, an rsantsar da sabon Shugaban kasar Mamahadu Issoufou a karkashin Janhuriya ta Bakwai, wanda kuma ya kawo karshen mulkin soja a kasar.Wannan ya kawo karshen gwamnatin mulkin soja ta watanni 14, karkashin jagorancin Janar Salou Djibo, wanda ya samu lamban yabon girka demokaradiya yayin bikin rantsuwan.Akwai shugabanni takwas daga sauran kasashen Afrika da suka halarci bikin wanda aka yi a Yamai babban birnin kasar ta Janhuriyar Nijar.Issoufou ya lashe zaben da aka yi watan jiya, inda ya samu kashi 58 cikin 100, tare da doke Tsohon PM Seini Oumarou yayin zagaye na biyu na zaben.Sabon Shugaban Mahamadou Issoufou ya yi alkawarin yakan talauci da ya addabi al’umar kasar. 

Mahamadou Issoufou Sabon Shugaban kasar Janhuriyar Nijar
Mahamadou Issoufou Sabon Shugaban kasar Janhuriyar Nijar AFP/ Boureima HAMA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.