Isa ga babban shafi
Nijar

Zaben sabon shugaban Janhuriyar Nijar

Yau Asabar masu zaben kasar Janhuriyar Nijar kimanin mutane milyan 6.7 ke kada kuri’ar zaban sabon shugaban kasa cikin shirin mayar da kasar kan turbar demokaradiya.Zaben shugaban kasar zagaye a biyu ana fafatawa tsakanin dadadden madugun ‘yan adawa Mahamadou Issoufou na jam’iyyar PNDS-Tarayya da tsohon PM Seini Oumarou na jam’iyyar MNSD Nasara, kuma nan da jimawa kadan ake bude tashohin zabe, da karfe takwas agogon kasar.Tun bayan juyin mulkin shekarar data gabata, da Janar Salou Dijabo ya kifar da gwamantin Mammadou Tandja, sakamakon takaddamar tazarce bayan karewar wa’adin Tandja. Gwamnatin ta mulkin soja ta dauki haramar mayar da kasar ta Janhuriyar Nijar tafarkin demakaradiya. 

AFP/RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.