Isa ga babban shafi
Niger

Zaben shugaban kasa a kasar jumhuriyar Nijar,yanayin kasar a yanzu.

ZABE A KASAR NIJARA dai ranar Assabar 12 ga watan Maris shekara ta 2011, za a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar ta jumhuriyar Nijar.Yan takara guda biyu za su fafafatawa :Mahamadou Issoufou na PNDS-Tarraya da Seini Oumarou daga bangaren jama’iyar MNSD-Nassara.TASSAWIRAR KASAR NIJARIdan muka dibi tassawirar kasar ta Nijar,ta da da fadin murabadin kilomita :milyon daya da dubu dari biyu da satin da bakoye(1.267.000 km2).Kasar ta kassance a tsakiyar yankin sahel,kishi 2 cikin 3 na kasar ya kassance hamada.Kasar ta yi iyaka da kasashe guda 7 da kuma dukansu ta fisu fadin kasa .Kasashen sun kada da :kasar Aljeriya,Libiya ,Cadi,Najeriya,Benin ,Burkina-Faso da Mali.Al’ummar kasar ta kai milyion 15da dubu dari biyu 2(15.2 00.000),da kuma ta kumshi kabilu manya-manya guda 9 : Haussawa sun kassance kabilu mafi yawa na kasar(Katsinawa,Gobirawa,Daurawa,Kufayawaa,Adarawa,Zanfarawa,Damagarawa,Tsotsebaki,Arawa,Gobawa da dai sauren su).An dai samun kabilun haussawa koina a cikin kasar ta Nijar.Sai dai sun fi yawa a cikin yankin kuncin kasar ,a cikin jahohi kamar Tawa,Maradi,Zinder (Damagaram). Bayan haussawa ana samun sauren kibilun a kasar ta Nijar da su ka hada da,Zabarmawa,Fulani,Gurmawa,Kanuri(Bare-Barin Borno),Larabawa,Abzinawa(Buzaye),Buduma,Tubawa da sauren kankanan kabilu.Yamai ita ce babban birnin kasar.Harshen da ake anfani da shi a cikin ma’aikatun bariki shi ne Turancin France(Faransanci).Kasar ta kumshi kishi 90 cikin 100 na musulmi.SIYASABayan samun incin kai daga kasar France a ranar 3 ga watan Ugusta na shekara ta 1960,shugaban kasar na farko shi ne Diori Hamani.Seyni Kountche ya gadeshi daga shekara ta 1974 zuwa ta 1987.Zaben farko kan tafarkin demokaradiya an zabi Mahamane Ousman shugaban kasa a cikin shekara ta 1993.A shekara ta 1995 an sa hannu domin kawo karshen takadama da yan tawaye abzinawa,wanda ta doki tsawon lokaci daga shekara ta1991 zuwa ta 1994.Janar Bare Mainassara ya gudanar da juyin mulki a shekara ta 1996.Shi kuma a shekara ta1999 aka kashe shi a cikin wani juyin mulki da Daouda Malam Wanke ya gudanar.An zabi Mamadou Tandja a matsayin shugaban kasa karkashin jama’iyar MNSD-Nassara.A shekara ta 2009 Mamadou Tandja ya wargazar da majalasar dokokin kasar tare da canza kundin tsarin mulkin kasar da wargazar da kotun tsarin mulki ta kasar.Salou Djibo ya gudanar da junyin mulki ga shugaba MamadouTandja watan Febriyeru na shekarata 2010.TATALIN ARZIKIKasar Nijar ta yi fama da yunwa har so 2,a shekara ta 1972 zuwa da shekara ta 1973 da kuma a shekara ta1984 zuwa shekarata 1985.Dokacin mutanan kasar na noma irin na galgajiya .Kasar Nijar ta kassance daya daga cikin kasashen duniya masu arzikin karfen Uranium.Uraium ya kassance babban arzikin da kasar ke tinkaho da shi da kuma a ke tonowa a cikin yankin arewacin kasar .BASHIA yanzu haka bankin duniya na biyar kasar bashin da ya kai milyon 966 na dallar Amurika a shekara ta 2008.SOJI DA TSAROA shekara ta 2010 kasar na da soji da yawan su ya kai dunbu 5 da dari 3(5.300) kamar yadda cibiyar nazari kan dubarun yaki ta sanar.Ta na da jami’an tsaro da su ka kai dubu 5 da dari 4(5.400).Kasar na fuskantar barazanar yan kungiyar Al’Qaida a yankin yammacin Afrika(AQMI) a cikin yan shekarunan.Lamari na baya-bayanan kan barazanar kungiyar Al’Qaida shi na kama ma’aikatan kanfanin AREVA guda 7 da kuma na ranar 7 ga watan janeru shekata ta 2011 da su ka kama wasu turawa yan kasar France guda 2, da su ka tarda ajalin su a wurin gwagormayar kwatosu,kan iyakar kasar da ta Mali .  

Janar Salou Djibo shugaban kasar Nijar
Janar Salou Djibo shugaban kasar Nijar AFP PHOTO/ISSOUF SANOGO
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.