Niger
Yan takarar shugabancin kasar Nijar guda 9 daga cikin 10 su nemi da a dage zaben shugaban kasar.
A game da zaben kasar jumhuriyar Nijar da zai gudana a ranar 31 ga wanan wata, kungiyar tarrayar turai ta sanar da turo masu sa iddo kan zaben guda 38. A daidai wanan lokaci,yan takarar shugabancin kasar guda 9 daga cikin 10,sun kira da daga zaben zuwa ranar 20 ga watan Febriyeru,wanan kuma a cikin wata wassika da su ka aikama shugaban kasar Janar Salou Djibo.Ba tare da wani jinkiri ba kai tsaye a rana daya shugaban mulkin sojin kasar Salou Djibo ya amsa da cewa, babu maganar dage wanan ranar zabe daga 31 ga wanan wata zuwa wata rana ta daban ko da kwana guda.
Wallafawa ranar: