Isa ga babban shafi
Tunisiya

Sabuwar Gwamnatin Tunisia na kussan rugujewa

Sabuwar gwamnatin kasar Tunisia ta na fuskantar rugujewa, bayan wasu ministoci sun yi murabus. Tuni shugaban kasar na wucin gadi da Praminista su ka bayyana murabus daga jam’iyyar RCD mai malki, kuma Praministan Mohammed Ghanouchi, ya tsaya kai da fata cewa ba su da hanu cikin murkushe masu zanaga-zanga, tare da cewa gwamnatin ta wucin gadi ta na bukatar masu kwarewa.Masu zanga-zangar sun bukaci wargaza jam’iyyar ta RCD baki daya, ministoci uku suka bayyana ficewa daga cikin sabuwar gwamnati.Ana daukan jam’iyyar ta RCD a matsayin alama ta tsohon shugaban kasar ta Tunisia Zine al-Abedine Ben Ali, wanda masu zanga-zanga suka tilasta masa ban kwana da madafun ikon kasar zuwa hijira a kasar Saudia. 

Masu zanga-zangar kyamar sabuwar gwamnatin kasar Tunisia
Masu zanga-zangar kyamar sabuwar gwamnatin kasar Tunisia REUTERS/Zoubeir Souissi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.