Isa ga babban shafi
Sudan

An nemi mahukuntan Sudan kan kare hakkin al'umma

Cibiyar tabbatar da demokaradiya, ta tsohon shugaban kaasr Amurka, Jimmy Carter, ta bukaci shugabannin kasar Sudan, da su kare 'yan kasar dake Arewaci da kudancin kasar, bayan zaben raba gardama.Cibiyar ta ce, ya dace shugabannin su kare 'yan kudancin kasar dake Arewa, da kuma Yan Arewacin kasar dake kudu, bayan zaben.Cibiyar ta kuma bukaci daina kamalai masu tada hankali daga kowanne bangare. Kasar ta Sudan tana shirin gudanar da zaben raba gardama game da sanin makomar yabkin kudanci, kamar yadda yarjejeniyar samar da zaman lafiya ta shekara ta 2005, wadda ta kawo karshen yakin basasan. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.