Isa ga babban shafi
SUDAN

Sojojin MDD ne za su tabbatar da tsaron kan iyakar Arewa da kudancin Sudan

Wani jami’in kasar Amurka ya ce sojojin majalisar dinkin duniya ne za su sanya ido don tabbatar da tsaro a kan iyakar Arewaci da Kudancin Sudan kafin kuri’ar raba-gardaman da za a gudanar.Wannan babban jami’in Amurka da ya ce baya so a bayyana sunansa ya kuma shaida wa manena labarai cewa za a iya kakabawa Sudan takunkumi idan ta yi jan-kafa wajen gudanar da kuri’ar raba gardamar.A lokacin da jakadun majalisar dinkin duniya suka ziyarci Sudan a makon da ya gabata ne, shugaban kudancin Sudan din Salva Kiir ya bukaci a kai dakarun kiyaye zaman lafiya kan iyakar.Tuni dai dama akwai wasu jakadun na majalisar ta dinkin duniya dake sanya idanu a yankin, wanda dukkan bangarorin ke zargin juna da jibge sojoji, gabanin kuri’ar raba-gardamar.  

Cibiyar bada horo ta majalisar dinkin duniya a Rejaf kudancin Sudan
Cibiyar bada horo ta majalisar dinkin duniya a Rejaf kudancin Sudan Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.