Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaban Faransa Sarkozy ya ce babu makawa wajen kawar da alka'ida

Tun bayan kisan da aka yi wa Michel Germaneau a yankin Sahel na Afrika, shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozi ya tura ministan harakokin wajensa Bernard Kouchner a yankin na Sahel, inda a jiya Litinin a birnin Nouakchott na kasar Mauritaniya ya tattauna da shugaban kasar Mohamed Ould Abdel Aziz, kafin a yau Talata ya ziyarci biranen Bamako na kasar Mali, da Niamey na Janhuriyar Niger.Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da ajiya Litanin ya tabbatar da mutuwar Michel Germaneau da 'yan ta’addan alka’idan reshen Magharib Aqmi suka yi garkuwa da shi, ya sha alwashin daukar fansa a kan kisan da ya kira na rashin imani,A cikin jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar ta kafar taTV a jiya, shugaba Sarkozy ya bayyana cewa yan tsageran ba tare da tausayi ba sun kashe tsohon dan shekaru 78 a duniya, wanda kuma ke fama da rashin lafiya, tare da hana masa shan maganin da yake bukata kafin su aikata mummunan aikin a kansa. 

Ministan Harkokin Wajwn Faransa Bernard Kouchner da shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Abdel Aziz, à Nouakchott, le 26 juillet 2010.
Ministan Harkokin Wajwn Faransa Bernard Kouchner da shugaban kasar Mauritania, Mohamed Ould Abdel Aziz, à Nouakchott, le 26 juillet 2010. AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.