Isa ga babban shafi
Zambia

Zambia Ta Zargi Kasar Netherlands

Jamiyyar dake mulki akasar Zambia ta zargi kasar Netherlands da daukan nauyin babban jamiyyar adawar kasar.Wannan zargi dai na barazana ga tallafin da kasar ke samu daga kungiyoyin waje wadanda suka daina baiwa kasar agajin na yaki da cutar tsida da sauran alamurran kiwon lafiya, saboda zargin cin hanci da rashawa.Babban Sakataren Jamiyyar, MMD dake mulkin kasar, Katele Kalumba ya fadi cewa Cibiyar Kulada Harkokin Jamiyyun Siyasa da Democradiyya dake kasar Netherlands, na tallafawa Jamiyyar PF karkashin jagorancin Michael Sata, wanda yake barazana ga Gwamnatin Shugaba Rupiah Banda.Ofishin Jakadancin kasar Netherlands dake Lusaka, ya fito fili ya karyata zargin.Bara, kasar Netherlands da Sweden suka hana baiwa kasar Zambia Dolan Amirka miliyan 33 gudunmawa domin yaki da cutar tsida, saboda zargin  wasu jamian Gwamnatin kasar da handame Dalan Amirka miliyan biyar. 

reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.