Isa ga babban shafi
Saudiyya

Matsayin Saudiyya kan bacewar dan jarida Khashoggi

Saudiyya ta ce za ta yi ramuwar gayya a game da duk wani takunkumi ko kuma wani mataki da za a dauka kan kasar, sakamakon zargin da ake yi ma ta na kashe Jamal Khashoggi dan jaridar da ya bata tun lokacin da ya shiga ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul.

Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiyya da ya bata a Turkiyya
Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiyya da ya bata a Turkiyya MOHAMMED AL-SHAIKH / AFP
Talla

A jiya asabar, shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki kan Saudiyya matukar aka tabbatar da cewa kasar na da hannu wajen bacewar dan jaridar,

Sanarwar da mahukuntan Saudiyya suka fitar ta hannun kamfanin dillancin labaran kasar, na cewa ba za su amince da duk wata barazana ba, sannan kuma a shirye suke domin mayar da martani a game da duk wani takunkumi da za a kakaba masu saboda wannan lamari na dan jaridar Khashoggi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.