Isa ga babban shafi
Amurka

Kungiyoyin da ke nuna kyama na karuwa a Amurka

A kasar Amurka adadin kungiyoyin da ke nuna kyama ga wani jinsi na jama’a ya karu da akalla kashi 4% a shekarar da ta gabata, kamar dai yadda wani rahoto da Cibiyar Southern Poverty Law Center ya nuna.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump 路透社。
Talla

Rahotan Cibiyar ya bayyana cewa adadin irin wadannan kungiyoyi da aka kafa domin nuna kyama ya kai 954 a shekara ta 2017, a maimakon 917 a shekarar da ta gabace ta wato 2016.

 

Wannan dai na nufin cewa adadin ya karu da akalla kashi 20% a cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma ana iya samun rassan wadannan kungiyoyi a cikin jihohin Amurka akalla 50.

 

Heidi Beirich, daraktan cibiyar da ta gudanar da binciken, ya dora alhakin karuwar masu irin wannan ra’ayi na nuna kyama ga gwamnatin Donald Trump, musamman lura da yadda kungiyoyi masu da’awar kare farar fata da masu kyamar baki ke cigaba da bayyana a lokacin mulkinsa.

 

Babban abin da ya firgata jama’a dangane da wannan rahoto shi ne, yadda gwamnatin ta Trump ba ta daukar wasu muhimman matakai domin takawa masu irin wannan da’awa birki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.