Isa ga babban shafi
Falasdinu

Abbas na son farfado da zaman lafiya a gabas ta tsakiya

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya bukaci shirya taron kasashen duniya a cikin wannan shekara don kaddamar da sabuwar fafutukar samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da kuma share hanyar kafa kasar Falasdinu.

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas AFP
Talla

A wani jawabi irinsa na farko da ya gabatar a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a jiya Talata, Abbas ya gabatar da sabon tsarin farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Sabon tsarin ya bukaci jingine Amurka a matsayin mai jagorancin shiga tsakani a tattaunawar tsakanin bangarorin biyu.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, matakin da ya harzuka al’ummar Falasdinu da ta ce ba ta amince da Amurka ta ci gaba da kasancewa mai shiga tsakanin ba.

Yanzu haka Abbas na bukatar kafa wani gungun kasashen duniya da zai jagoranci sasanta rikicin Yahudawa da Faladinawa.

A cewar Abbas, taron da ya bukaci gudanar da shi nan gaba a cikin wannan shekara, zai samu halartar mambobi na din-din-din a Kwamitin Sulhu da suka hada da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka da kuma Kungiayr Kasashen Turai da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.