Isa ga babban shafi
UN

An fara taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York

Yau ne ake fara taron Majalisar Dinkin Duniya na bana, inda ake ganin rikicin Syria da kuma takaddamar shirin nukiliyar Iran, zasu mamaye taron. Shugaba Mahmud Ahmadenajad na kasar Iran, ya zargi shugabanin Yammacin duniya da karya dokokin na duniya, inda yayi watsi da barazanar da Isra’ila keyi na kaiwa kasar hari. Ana saran Shugaba Barack Obama, zai yi jawabi ga Majalisar yau, yayin Sakatariyar sa ke ziyarar wasu kasashen Musulmi dan kwantar da hankalin su kan fim din da ya haifar da zanga zangar kiyaya ga Amurka.  

Hedkwatan Majalisar Dinkin Duniya, a birnin New York.
Hedkwatan Majalisar Dinkin Duniya, a birnin New York. Getty Images
Talla

A bangare daya kuma, Faransa na neman goyin bayan ganin Majalisar ta amince ta shirin amfani da karfin soji a Mali.

Shugaba Obama na daya daga cikin wadanda ake sa ran za su fara gabatar da jawabi a taron.

Wannan jawabi kuma ana ganin dai shi ne jawabinsa na karshe a gaban taron kamin a gudanar zaben kasar ta Amurka, inda zai yi kwana daya ne kawai a birnin New York ba tare da ya gana da sauran shugabannin duniya ba.

Har ila yau, a taron na Majalsiar Dinikin Duniya, za a gudanar da wani taro akan Jamhuriyar Demoradiyyar Congo inda da shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame, wanda yake musanta zargin marawa ‘Yan tawyen baya, za su gana tare da shugaban kasar Congon, Joseph Kabila.

A yayin da ake sa ran taron, zai karawa sabon shugaban kasar Somalia, Hassan Sheikh Mahmoud, kwarin gwiwa na ganin ya dauki matakan gaggawa, idan har yana so kada kasar ta Somalia ta shiga wani hali.

Haka kuma, Firaministan kasar Birtaniya, David Cameron, da shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf har ila yau da shugaban kasar Indonesia, Susilo Bambang Ydhoyono za su shata sabbin muradin cigaba a yayin da wa’adin da aka sa na shekarar 2015 ke karatowa.

Akalla shugabannin kasashe, da jami’an gwamnatoci da kuma Ministoci daga sassa daban daban na duniya sama dari ne ake sa ran za su halarci taron inda a yau za su fara tattaunawa akan bin doka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.