Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Kananan yara 163 suka rasa rayukansu sakamakon shakar guba a Zamfara

Wallafawa ranar:

A Najeriya hukumomi sun bada tabbacin mutuwar kananan yara da dama a jihar Zamfara, dake arewacin kasar, sakamakon shakar gubar dalma da sukeyi. Wannan matsalar dai ta faru ne a yankuna daban-daban na kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar ta Zamfara, inda a ranar daya ga watan yunin shekarar dubu biyu da goma, hukumomin jihar suka soma aikin kwashe kasar da sukace tanada gubar zuwa wani wurin da ake tunanin ba zata cutawa kowa ba.Matakin dai hukumomin sunce sunyishi ne domin magance yaduwar cutar zuwa wasu sassan jihar.Gadai rahoton da wakilin mu a Sakkwato Faruk Muhammad Yabo, ya aiko mana.

Mahakar Dalma ba bisa ka'ida ba
Mahakar Dalma ba bisa ka'ida ba
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.