Shirin dandalin fasahar Fina-finai, Wanda ni Hauwa Kabir ke gabarwa, a wannan Makon shirin yayi hira ne da wasu fitattun jarumai da suka nuna bajintar su a wani sabon film din da, babban daraktan shirya fina-fainai na Kanny Wood wato Hassan Giggs yayi alkawin shirya wa a farkon wannan shekara na 2018, in da ya ce Film din zai zama sharan fage ga cin nasarar Kanny Wood a idanun duniya dama wasu masana’antar shirya fina-finai, wadanda suka hada harda su Holly Wood baki daya. Haka ya sa na garzaya masana'antar domin gane wa idanuna domin gaskata zancen sa.