Amurka ta janye daga yarjejeniya Paris
Kasashen duniya sunyi tir da matakin da shugaban Amurka ya dauka na janye kasar daga yarjejeniyar rage dumamar yanayi da aka cimma a watan disambar 2015 a birnin Paris.
Trump ya ce ya dauki wannan mataki ne lura da irin illolin da yarjejeniyar za ta haifar wa tattalin arzikin Amurka. To sai dai tsohon shugaban kasar Barack Obama da sauran manyan kasashen duniya sun yi allawadai da wannan mataki da Trump ya dauka.