Isa ga babban shafi

Sabon yaki na barazanar barkewa kan Syria

Wakilan Rasha da Turkiya sun gana ranar Juma’a domin yayyafawa wutar yakin dake neman tashi a tsakaninsu ruwa, biyo bayan farmakin jiragen yakin sojin Syria, da ya kashe dakarun Turkiya 33 a lardin Idlib ranar Alhamis.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiya Racip Tayip Erdogan
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiya Racip Tayip Erdogan Alexey DRUZHININ / SPUTNIK / AFP
Talla

Tun a ranar Alhamis din ne dai rundunar sojin Turkiya ta maida raddi kan kashe sojojin nata, inda ta kaiwa cibiyoyin sojin Syria akalla 200 farmaki, tare da halaka dakarun kasar 16.

Kafin tattaunawar neman sulhun ta Jumma'a ta gudana kuma, sai da aka yi musayar zafafan kalamai tsakanin Rasha dake marawa sojin Syria baya da kuma Turkiyan, inda Rashan ta ce dakarun Turkiyan da jiragen yakin Syria suka halaka na taimakawa mayakan ta’adddan dake kasar ne, zargin da Turkiya ta yi watsi da shi, tare da neman haramta shawagin jiragen sama a lardin Idlib dake arewacin kasar ta Syria, yanki na karshe dake hannun yan tawaye.

Turkiyan ta kuma yi barazanar baiwa ‘yan gudun hijira damar kwarara zuwa nahiyar Turai, wadanda a baya ta killace, muddin kasashen yammacin Turai basu tsawatarwa Rasha da Syria kan sabbin hare-haren da suke kaiwa yankunan ‘yan tawayen kasar ba.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar barazanar kazancewar sabon yaki a Syria na karuwa a duk bayan sa’a 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.