Isa ga babban shafi

Newcastle ta hana musabaha saboda Coronavirus

Kungiyar Kwallon kafar Newcastle dake Ingila ta haramta musabaha ko kuma shan hannu lokacin gaisuwa domin kaucewa kamuwa da cutar coronavirus.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa na Newcastle
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa na Newcastle Reuters
Talla

Mai horar da Yan wasan kungiyar Steve Bruce yace sakamakon shawarar likita, sun haramtawa Yan wasa da kuma Yan kallo musabaha domin kaucewa yaduwar cutar wadda aka tabbatar da cewar ta shiga Birtaniya.

Manajan yace suna sa ido a talabijin da kuma sauraron rediyo domin jin halin da ake ciki dangane da wannan cutar wadda ta zama annoba a kasashen duniya da dama, ganin yadda take dibar rayukan jama’a.

Shima manajan kungiyar Liverpool Jurgen Klopp yace suna daukar barazanar cutar da muhimmanci amma ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga kungiyar.

Cutar coronavirus ta haifar da soke wasanni da dama a kasashe daban daban, cikin su harda gasar Serie A a Italia, wanda aka soke karawa 5 ciki harda na kungiyoyin Juventus da Inter Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.