Isa ga babban shafi
China

Annobar cornavirus na cigaba da tafka barna a ciki da wajen China

Adadin Mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus a China ya kai 2,715, yayin da cutar ta kama mutane sama da 78,000.

Wani misalin fasalin kwayar cutar murar mashako ta coronavirus da masana kimiyya suka fitar.
Wani misalin fasalin kwayar cutar murar mashako ta coronavirus da masana kimiyya suka fitar. NEXU Science Communication/via REUTERS
Talla

A kasar Koriya ta Kudu ma an samu karuwar masu dauke da cutar, inda suka zarce 1,000 cikin su harda sojin Amurka.

Koriya ta Kudu ce ke matsayin kasa ta biyu inda annobar ta fi shafar jama’a.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar lafiya a kasar Iran ta tabbatar da mutuwar mutane 15 yayin da wasu 95 ke jinya, ciki har da mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar.

Shugaban Hukumar lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya gargadi kasashe da su kasance cikin shirin yiyuwar barkewar annoba, lura da cewa tuni Coronavirus ta shafi kasashe masu tarin yawa.

A yankin Turai cutar ta fi tsananta ne a Italiya mai majinyata akalla 283, yayin da a karon farko aka ruwaito cutar ta bulla a kasashen Austria, Croatia da kuma Switzerland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.