Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta daina karbar haraji daga Amurka saboda Coronavirus

Gwamnatin China ta sanar da shirinta na kauce wa karbar harajin kayyakin jinya da Amurka ke shigo mata da su, duk da yakin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da China ke fafutukar yaki da cutar Coronavirus.

Wasu daga cikin malaman jinyar da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus a China
Wasu daga cikin malaman jinyar da ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus a China STR / AFP
Talla

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da liktoci da malaman jinya ke kula da dimbin masu dauke da cutar Coronavirus a asibitoci, yayin da suke fama da karancin kayayyakin jinya.

Daga cikin kayayyakin da China ta ce ba za ta karbi harajinsu ba, sun hada da na’urar gwajin marasa lafiya da nu’urar musayar jini ko kuma gwajin jinin.

Yanzu haka wadannan kayayyaki na cikn jerin hajojin Amurka 969 da suka cancanci kauce wa karbar haraji a kansu a China.

Sauran kayayyakin sun hada da alkama da dawa da masara da daskararren namen alade da naman shanu da waken suya, sai kuma man diesel da man fetur da kuma wasu nau’ukan karafa kamar jan gaci.

A cewar gwamnatin China, matakin kin karbar harajin wadannan kayayyaki na da nasaba da yunkurin saukake wa al’ummar kasar abubuwan da suke bukata.

Sama da mutane dubu 72 suka gamu da cutar Coronavirus a China, yayin da mutane dubu 1 da 800 suka rasa rayukansu a sanadiyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.