Isa ga babban shafi
Amurka-Jamus

Amurka da Jamus sun tatsi bayanan sirrin kasashe na gwamman shekaru

Hukumomin leken Asirin Amurka da na Jamus sun tatsi bayanan asirin wasu gwamnatocin kasashen duniya a tsawon gwamman shekaru ta hanyar amfani da wani boyayyen kamfani da ke karkashin ikonsu.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel. 路透社
Talla

Kamfanin mai suna Crypto AG na kasar Switzerland na kan gaba wajen rarraba na’urorin nadar bayanan sadarwa a wasu kasashen duniya 120 tun bayan kawo karshen yakin duniya na II zuwa farkon wannan karni da muke ciki.

Daga cikin kasashen da lamarin ya shafa har da Iran da India da Pakistan da kuma gwamnatocin kasashen kudancin Amurka.

Wadannan kasashe ba su da masaniyar cewa, kamfanin na Crypto AG mallakar Hukumar Leken Asiri ta Amurka ce tare da hadin guiwar takwarata ta Jamus.

Kasashen biyu sun yi amfani da na’urorin kamfanin Crypto domin samun damar kutsawa cikin kundin kamfanin cikin sauki da zummar karanta sakwannin gwamnatocin kasashen na duniya kamar yadda jaridar Washington Post ta Amurka da kafar Talabijin ta ZTE ta Jamus har ma da kafofin yada labaran gwamnatin Switzerland suka rawaito.

Jaridar Washington Post ta bayyana wannan al’amari a matsayin juyin mulkin leken asiri da aka gani a wannan karni.

A bangare guda, bayanai sun ce, Crypto AG ya samu ribar miliyoyin Dala, kuma daga bisani kudaden sun tafi cikin asusun hukumar leken asirin Amurka ta CIA da kuma hukumar BND ta Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.