Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

Annobar Coronavirus ba ta mamaye duniya ba - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce shu’umar cutar nan ta Corona virus da ta barke a China, ta kuma yadu zuwa wasu kasashe sama da ashirin, ba ta kai munzulin da za a kira ta annobar da ta mamaye duniya baki daya ba.

Wani ma'aikacin filin tashi da saukar jiragen sama a Paris sanye da kariya don gudun kamuwa da cutar Coronavirus
Wani ma'aikacin filin tashi da saukar jiragen sama a Paris sanye da kariya don gudun kamuwa da cutar Coronavirus Alain JOCARD / AFP
Talla

Shugabar sashen da ke kula da cututtuka masu yaduwa na Hukumar Lafiya ta Duniyar, Sylvie Briand, ta shaida wa maneman labarai a birnin Geneva cewa yanzu dai ana matsayi ne da za a ce cutar ta zama annobar da ta yadu zuwa wasu kasashen duniya.

Wannan cuta ta corona virus ta halaka sama da mutane 425, mutane sama da dubu 20 sun harbu da ita a China, kuma kusan dukkanninsu na rayuwa ne a lardin Hubei da ke tsakiyar kasar, sannan cutar ta yadu zuwa kasashe sama da 24 tun da ta bulla a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Briand ta ce yayin da cutar ke yaduwa cikin sauri a lardin Hubei, a wajen lardin wadanda suka harbu da cutar ‘yan kalilan ne, kuma yaduwar ba ta taka kara ta karye ba, inda ta ce a wadannan wurare, kokarin da ake shine na dakile yaduwarta, haka ma yake a kasashen da cutar ta tsallaka.

Hukumomi a China sun dauki kwararan matakan dakile wannan cuta, mai shafar numfashi, yayin da sauran kasashen da annobar ta afka musu suke bin sahu ta wajen daukan matakan hana ta yaduwa.

Hukumar Lafiyar ta Duniya ta shawarci jama’a da su lizimci wanke hannuwansu da kyau, saboda sanya kyallayen kariya a fuska ba zai bada wadatacciyar kariya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.