Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka-Sahel

Faransa na kokarin shawo kan Amurka game da Sahel

Ministar Tsaron Faransa, Florence Parly na ziyara a birnin Washington da zummar shawo kan hukumnomin Amurka don ganin sun amince da ci gaba da wanzuwar sojojin kasar a yankin yammacin Afrika mai fama da hare-haren ta’addanci.

Sojojin Amurka na taka muhimmiyar rawa a cikin rundunar Barkhane da Faransa ke jagoranta a Sahel
Sojojin Amurka na taka muhimmiyar rawa a cikin rundunar Barkhane da Faransa ke jagoranta a Sahel RFI/Olivier Fourt
Talla

Ziyarar Ministar na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan Faransa ke fuskantar matsin lamba bayan shafe shekaru suna kokarin karfafa dakarun da ke fada da masu tsattsauran ra’ayi.

A ‘yan kwanakin nan ne, Ministar ta yi ran-gadi a yankin Sahel, inda gwamnatocin kasashen yankin ke da karancin karfin hana tashe-tashen hankula, abin da ya bai wa mayakan jihadi damar cin karansu babu babbaka.

Gwamnatin Faransa da kawayenta na kallon Sahel a matsayin yankin mai muhimmanci da za a iya amfani da shi wajentunkarar barazanar mayakan jihadi da kuma dakile bakin hauren da ke kwarara cikin Turai ta tekun Mediterranean.

Amurka na cikin aminan Faransa da suka sanya dakarunsu cikin rundunar Barkhane wadda Faransa ke jagoranta a Sahel, inda suke musayar bayanan sirri da juna, yayin da suke kashe kimanin Dala miliyan 45 kowacce shekara.

Wani babban jami’i a fadar gwamnatin Faransa ya shaida wa AFP cewa, Amurka na da muhimmanci a Sahel, lura da gagarumar rawar da take takawa a yanki, kuma babu wanda zai iya maye gurbinta a cewar Jami’in.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.