Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Dubban 'yan Iraqi na zanga-zangar neman korar dakarun Amurka

Dubban magoya bayan fitaccen malami a Iraqi Moqtada al Sadr, na gudanar da zanga-zanga a birnin Bagadaza yau Juma’a, inda suke neman tilastawa sojojin Amurka ficewa daga kasar.

Dubban 'yan Iraqi magoya bayan fitaccen malami Moqtada al-Sadr, yayin zanga-zangar neman korar sojojin Amurka daga kasar, a birnin Bagadaza. 24/01/2020.
Dubban 'yan Iraqi magoya bayan fitaccen malami Moqtada al-Sadr, yayin zanga-zangar neman korar sojojin Amurka daga kasar, a birnin Bagadaza. 24/01/2020. Reuters
Talla

Sabuwar zanga-zangar dai tamkar fami ce ga wadda dubban ‘yan kasar ta Iraqi suka shafe makwanni sama da 10 suna yi kan neman Fira Ministan Adel Abdul Mahadi yayi murabus, da yiwa gwamnatin kasar garambawul, da kuma yakar matsalar cin hanci.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewar, zanga-zangar kin jinin sojojin Amurkan ta fi zafafa a yankin Jadiriyah dake gabashin Baghdad, inda suke kwarmata kalaman bayyana dakarun na Amurka da kawayensu a matsayin ‘yan mamaya.

Kimanin sojojin Amurka dubu 5 da dari 200 ne yanzu haka ke jagorantar yakar ta’addanci a Iraqi, to sai dai gwamnatin Iraqi ta ce matakin kashe Qasem Soleimani, daya daga cikin manyan kwamadojin Iran a birnin Bagadaza, ya kawo karshen damar da ta baiwa sojin Amurka na zama a kasar.

A farkon watan Janairu majalisar kasar Iraqi ta kada kuri’ar amincewa da kudurin korar sojojin Amurka, saboda keta mata haddin ‘yanci da Amurkan tayi, ta hanyar kai farmakin sojin da ta kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani ba tare da neman izinin daukar mataki acikin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.