Isa ga babban shafi
Rasha

Shugaba Putin ya nada wasu ministoci a gwamnatin Rasha

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya sake nada wasu tsoffin Ministocinsa da ya sauke kasa da mako guda a cikin sabuwar Gwamnatin da yake shirin kaddamar, bayan sanarwar da yayi na sabbin sauye-sauye .

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Sergei Lavrov Ministan waje da kuma Sergei Shoigu Ministan tsaro , dukkaninsu masu karfin fada aji sun sake hawa kujeransu.

Har ila yau akwai Ministan kudi Anton Siluanov da Ministan Makamashi Alexander Novak duk suna cikin sabuwar Gwamnatin Rashan.

Kusan mako daya kenan da Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gabatarwa da majalisar kasar kudurin neman yin zaben raba gardama kan yiwa wasu sassan kundin tsarin mulki kwaskwarima, domin karfafa ayukan ‘yan majalisar.

Putin ya gabatar da wannan kuduri ne, yayin jawabi kan lamuran kasa, da ya saba gabatarwa a zauren majalisar kasar duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.