Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 15/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 19/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 19/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

Adadin attajiran duniya ya rubanya - Oxfam

media Shugabar Jamus Angela Merkel a taron DAVOS REUTERS/Arnd Wiegmann/File Photo

Kungiyar Agaji ta Oxfam ta fitar da wani sabon rahoto da ke cewa, adadin attajiran duniya ya rubanya a cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da mutane 22 da ke kan gaba wajen arziki suka mallaki kudin da ya zarce abin da matan nahiyar Afrika ke da shi.

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin kasashen duniya ke shirin gudanar da taron tattalin arziki na Davos.

Kungiyar Oxfam ta fitar da rahoton ne da zummar rokon shugabannin kasashen duniya da ke halartar taron tattalin arziki na Davos a duk shekara, da su dauki batun rashin daidaito ta fannin tattalin arziki da muhimmanci.

Shugaban kungiyar ta Oxfam reshen kasar India, Amitabh Behar ya ce, tattalin arzikin duniya na kunshe ne a cikin aljihun wasu attajirai da ‘yan kasuwa, abin da ya sa talakawa ke shakkun wanzuwar ire-iren wadannan attajirai a duniya.

Behar ya kara da cewa, mata da ‘yan mata na cikin dimbin mutanen da ba sa amfana da sabon tsarin tattalin arzikin duniya.

Ana sa ran akalla attajiran duniya 119 da suka mallaki jumullar Dala biliyan 500 su halarci taron na Davos na wannan shekarar kamar yadda kafar Bloomberg ta rawaito, kuma akasarin attajiran sun fito ne daga Amurka da India da kuma Rasha.

Oxfam ta ce, wani karamin gungun attajirai ne ya mallaki tiriliyoyin Daloli kuma akasarinsu maza ne.

Oxfam ta kara da cewa, arzikin da wadannan mutane suka mallaka ya wuce kima, yayin da kuma suke ci gaba da juya tattalin arzikin duniyar a tafin hannunsu duk da karancinsu.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure