Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Zafi zai fi tsananta a 2020 da kuma shekaru masu zuwa - MDD

Wani sabon rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana shekaru 10 da suka gabata, a matsayin lokacin da duniya ta fi fuskantar tsananin zafi da sauran matsaloli masu alaka da sauyin yanayi.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana 2016 a matsayin shekarar da zafi yafi tsananta a sassan duniya cikin shekaru 10.
Majalisar dinkin duniya ta bayyana 2016 a matsayin shekarar da zafi yafi tsananta a sassan duniya cikin shekaru 10. Reuters
Talla

Sai dai rahoton yayi gargadin cewar, tsananin zafin, da kuma tasirin sauyin yanayin kan aukwar lamurra masu alaka da shi, za su fi muni cikin wannan shekarar, da kuma masu zuwa a nan gaba.

Sashin majalisar dinkin duniya mai lura da yanayin ya tattara sakamakon bincikensa ne ta hanyar la’akari da yadda sauyin yanayi ya haddasa karuwar tsananin zafi a sassan duniya da kuma aukuwar masifun da suka hada da ambaliyar ruwa, tashin wutar daji da ta kone miliyoyin kadada na fadin kasa da kuma narkewar manya manyan curin kankara dake yankuna masu tsananin sanyi.

Binciken masana yanayin ya kuma bayyana 2019 da ta gabata a matsayin shekarar da zafi yafi tsananta a sassan duniya, baya ga shekarar 2016 dake kan gaba a tsawon shekaru 10 da suka gabata.

Masanan sun kuma ce wutar dajin da ta rika tashi a baya bayan nan cikin dazukan sassan duniya, ta tafka barnar kone fadin kasar da ya zarta kadada miliyan 10, kwatankwacin fadin kasar da ya zarta kasar Korea ta Kudu ko kuma Portugal. Zalika wutar dajin ta kuma kone gidaje da sauran gine-gine sama da dubu 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.