Isa ga babban shafi
Erdogan-Libya

Zan koya wa Haftar darasi a Libya- Erdogan

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin ladabtar da Khalifa Haftar na Libya matukar yaci gaba da kai hare-hare sassan kasar, bayan da ya yi watsi da tayin yarjejeniyar zaman lafiya a taron da ke gudana a Moscow.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. Murat Cetinmuhurdar/Presidential Press Office/Handout/REUTERS
Talla

A jawabin da ya gabatar kai tsaye ta gidan Talabijin bayan ficewar Haftar daga Moscow, Erdogan wanda ke mara baya ga gwamnati mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ya ce baza su lamunci salwantar da rayukan dubban jama’a a kasar ta Libya ba.

A cewar Erdogan, za su tattauna kan batun yayin taron da zai gudana a Berlin wanda wakilan Majalisar dinkin duniya da na kungiyar tarayyar turai da tarayyar Afrika baya ga kasashen larabawa za su halarta.

Kalaman na Erdogan dai karara ya bayyana yadda shugaban na Turkiya ya hasala da Haftar wanda ya ce a farko ya amince da sanya hannu a yarjejeniyar amma daga bisani ya yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.