Isa ga babban shafi
Iran

Dubban Iraniyawa sun halarci jana'izar Janar Soleimani

Dubban Iraniyawa sun yi dandazo a birnin Tehran na Iran domin gudanar da jana’izar kwamandan sojin kaar, Janar Qasem Soleimani da Amurka ta kashe a wani harin sama a Iraqi.

Mahalarta jana'izar Janar Soleimani a birnin Tehran
Mahalarta jana'izar Janar Soleimani a birnin Tehran Atta KENARE / AFP
Talla

Jagoran addini a kasar, Ayatollah Khamenei ya jagoranci sallar jana’izar marigayin, inda yake zubar da hawaye a yayin jana’izar.

Jama’a da dama sun yi ta rusa kuka, wasu na rike da hotunan marigayin, wasu kuma na yin tofin ala-tsine ga Amurka a wurin jana’izar.

Zainab Soleimani wadda ta kasance ‘ya ga marigayin, ta gargadi Amurka kan abin da zai biyo baya, tana mai bayyana shugaba Donald Trump a matsayin mahaukaci, sannan ta ce masa “ kar ka zaci komai ya kare bayan shahadar mahaifina”

Bayan gudanar da jana’izar, za a wuce da gawar zuwa Qom, daya daga cikin cibiyoyin Shi’a a kasar, kafin daga bisani a binne marigayin a mahaifarsa ta Kerman a gobe Talata.

Kasar Iran ta lashi takobin daukar matakin ramuwar gayya mai tsanani kan Amurka, yayin da a ranar Lahadi ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Ana kallo Janar soleimani tamkar gwarzo a Iran, yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin na biyu wajen karfin fada-a-ji bayan jagoran addinin kasar, Khamenei.

Marigayi Janar Soleimani mai shekaru 62, ya jagoranci aikin sojin Iran a yankin gabas ta tskiya, amma Amurka na kallon sa matsayin dan ta’adda.

Shugaba Trump ya ce, Soleimani na kitsa kai hari kan jakadun Amurka da dakarun sojinta da ke Iraqi da wasu sassa a yankin gabas ta tskiya.

Amurka ta yi amfani da jirgi mara matuki wajen kaddamar da farmakin da ya kashe Soleimani a ranar Juma’a a Iraqi bayan shugaba Trump ya bayar da umarnin halaka shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.