Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Majalisar Iraqi ta amince da kudurin korar sojin Amurka

Majalisar Iraqi ta amince da kudurin kora ko neman ficewar sojojin Amurka daga kasar, saboda keta mata haddin ‘yanci da Amurkan tayi, ta hanyar kai farmakin sojin da ta kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani ba tare da neman izinin daukar mataki acikin kasar ba.

Zauren majalisar kasar Iraqi.
Zauren majalisar kasar Iraqi. AFP / AHMAD AL-RUBAYE
Talla

Fira ministan Iraqi Adel Abdul Mahadi da kansa ne ya jagoranci zaman majalisar, inda ya marawa ‘yan majalisa 168 daga cikin 328 baya, wajen amincewa da bukatar sojin Amurka da kawayensu, tattara na ya nasu su bar kasar, saboda abinda suka kira kisan gillar siyasar da Amurka ta yiwa Iraqi.

Matakin majalisar ta Iraqi dai na zuwa ne bayan da mayakan sa kai masu biyayya ga Iran dake Iraqi, suka yi barazanar kaiwa sansanonin sojin Amurka hare-hare, tare da umartar dakarun kasar ta Iraqi su nisance su, biyo bayan halaka babban kwamandan dakarun juyin juya halin Iran a kasashen ketare a birnin Bagadaza.

A daren ranar asabar 4 ga watan Janairu aka kaiwa wani sansanin sojin Amurka, da kuma ofishin jakadancin kasar a Bagadaza farmaki da makaman roka, abinda ya fusata shugaban Amurka Donald Trump, wanda yayi barazanar kai hare-hare har kashi 52 a sassan Iran.

Akalla sojojin Amurka dubu 5 da 200 yanzu haka ke Iraqi inda suke taimakawa jami’an tsaron kasar ta fuskoki daban daban ciki har da basu horo, don dakile yiwuwa sake bullar mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.