Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na fuskantar tuhumar tsige shi daga karaga

Kwamitin Shari’a na Majalisar Wakilan Amurka da jam’iyyar Democrat ke da rinjaye, ya kaddamar da tuhume-tuhumen da za su kai ga tsige shugaban kasar Donald Trump daga karagar mulki.

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Loren Elliott
Talla

Ayar dokar farko da shugaban kwamitin Jerry Nadler ya gabatar, ta zargi Trump da karya ka’idojin mulki, yayin da ayar doka ta biyu ta zarge shi da hana Majalisar Dokokin Kasar gudanar da aikinta.

Bayanai na cewa, shugaba Trump ya hana bayar da tallafi ga kasar Ukraine domin wasu dalilai na siyasar cikin gida.

Sai dai Trump na ci gaba da musanta aikata lafi, yayin da ya yi watsi da shirye-shiryen tsige shi tare da alakanta shirin da hauka.

Muddin Kwamitin Shari’ar ya kada kuri’ar amincewa da ayoyin biyu na tuhumar Trump a cikin wannan mako, to babu shakka za a gabatar da ayoyin dokar ga zauren Majalisar Wakilan domin kada cikakkiyar kuri’a.

Da zaran Majalisar Wakilan ta amince, to ita ma Majalisar Dattawa wadda jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikiinta, za ta tuhumi shugaba Trump, watakila nan da farkon watan Janairu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.