Isa ga babban shafi
Duniya

Ko an dinke baraka tsakanin kasashen NATO a taron Ingila ?

Shugabannin Kasashen dake cikin kungiyar NATO za suyi kokarin dinke barakar dake tsakanin yau, a taron dake dada nuna rarrabuwar kawuna sakamakon rashin jituwa da kuma makomar kungiyar dake cika shekaru 70.

Kungiyar tsaro ta NATO
Kungiyar tsaro ta NATO REUTERS/Johanna Geron
Talla

Irin wannan taro da aka yi na shugabannin bara ya karkare da rashin fahimtar juna, inda shugaba Donald Trump na Amurka ya bukaci takwarorin sa na Turai da su dinga biyan kudaden da aka gindaya musu abinda ya sa shi karo da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Shugaba Macron ya bukaci sake tattaunawa da Rasha da kuma bukatar Turkiya da tayi bayani kan dalilin da ya sa ta kaiwa dakarun Kurdawan Syria hari da kuma sayen makamai daga Rasha.

A jiya, shugabannin sun gudanar da tarurruka daban daban a tsakanin su, kafin daga bisani suka ci abincin dare da Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta biyu a Fadar Buckingham, amma shugaba macron bai janye matsayin sa ba na cewar kungiyar ta kauce hanya, yayin da Trump ke cigaba da jaddada matsayin san a ganin kowacce kasa ta biya kudin ka’idar da aka gindaya mata.

Ana saran yau shugabannin su taru a otel din dake Watford a Arewacin London na sa’oi 3, kafin bayyana matsayin da suka cimma, yayin da ake saran Firaminista Boris Johnson yayi kiran inganta hadin kai a tsakanin su.

Fadar Firaministan tace Johnson zai jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin kasashen 29 ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.