Bayanai na nuna fara sauraron zarge-zargen a bainar jama'a da ake yiwa Trump kai tsaye ta kafofin Talabijin ake nunawa duniya.
Wannan al’amari na daga cikin manyan kalubalen dake fuskantar Shugaba Trump a tsawon shekaru uku da yayi bisa madafun iko yanzu haka.
Sama da wata guda kenan ana ta daukan matakan ganin an tsige Donald Trump.
Bayan zaman a bainin jama'a ne wakilan majalisar Dattawa za su jefa kuri'ar amincewa da matakin da aka dauka kafin zartasda tsige shi.
Manyan zarge-zargen da ake yi wa Trump kan fito ne daga wasu bayanan sirri da ake samu na kauce hanya wajen mulkin da yake yi.