Isa ga babban shafi
Faransa

Siyasar duniya na cikin rikici- Macron

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa, tsarin siyasar duniya na fama da matsanancin rikici, inda ya bukaci kafa sabbin nau’ukan hadaka domin magance matsalolin da duniya ke fama da su. Macron ya yi wannan gargadin ne a taron zaman lafiya da ke gudana a birnin Paris.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Gargadin da shugaba Macron ya yi na zuwa ne kwanaki kalilan bayan Mujallar Economist ta wallafa wata hira da ta yi da shi, inda yake cewa, kungiyar tsaro ta NATO na fama da shure-shuren mutuwa, sannan kuma kasashen Turai na fuskantar barazanar rasa karsashinsu.

Wadannan Kalamai na Macron sun aika sakawanni masu zafi ga shugabannin kasashen Turai, inda shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce, kalamansa sun yi tsauri.

Shugaban wanda ya nemi shahara a fagen siyasar duniya tun bayan darewarsa karagar mulki a shekarar 2017, ya ce, ana bukatar samar da sabbin hanyoyin hadin-kai tsakanin kasashen duniya da kungiyoyi, yana mai cewa ita ma kanta Majalisar Dinkin Duniya na fama da matsaloli.

Macron ya ce, tsarin tafiyar da siyasar duniya da kuma hada-hadar kudade ya samu tagomashi cikin shaker 70 , wato bayan kawo karshen yakin duniya na II, amma a yanzu wannan tsarin na cikin rikici.

Macron ya ce, shiru ba zai magance wannan kalubale ba, yayin da kuma ya sake yin gargadi kan yadda ake yin biris wajen tuhumar wasu cibiyoyin kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.