Shugaban kwamitoci 3 dake bincike shugaba Trump yace binciken da suke gudanarwa ya nuna musu cewar akwai alamun jami’in na da hannu wajen ingiza shugaban da wakilin sa Rudolph Giuliani da kuma wasu mutane wajen hana bada taimakon tsaro na kusan Dala miliyan 400 ga Ukraine har sai ya amince ya biyawa Trump bukatun san a siyasa.
Yanzu haka dai Mulvaney ne jami’i mafi girma da kwamitin ya gayyata domin gurfana a gaban sa ranar juma’a.