Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta janye daga yarjejeniyar Paris

A hukumance, kasar Amurka ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya matakinta na janyewa daga yarjejeniyar yaki da dumamar yanayi da kasashen duniya suka cimma a birnin Paris. Tuni manyan kasashen duniya suka fara bayyana damuwarsu kan wannan mataki na Amurka.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka NICHOLAS KAMM / AFP
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gaban kansa wajen janye kasarsa daga wannan yarjejeniya duk da kwararan shaidun da ke nuna irin girmar illar da dumamar yanayi ke yi wa duniya.

A cikin wasikar da ta aikewa Majalisar Dinkin Duniya, gwamnatin Amurka ta ce, za ta fice daga cikin wannan yarjejeniya dungurungum a ranar 4 ga watan Nuwamban shekarar 2020, wato kwana guda da kammala zaben shugabancin Amurka, inda shugaba Trump ke fatan yin tazarce.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya jaddada ikirarin Trump na cewa, yarjejeniyar ta birnin Paris za ta yi illa ga harkokin kasuwancin kasar ta Amurka.

Tuni shugaban Faransa, Emmanuel Macron wanda ya yi yi kokarin shawo kan Trump don ganin ya ci gaba da mutunta yarjejeniyar, ya bayyana damuwarsa kan matakin, yayin da Rasha ta ce, janyewar Amurkar zagon kasa ne ga yarjejeniyar.

Ita ma China ta nuna damuwarta a daidai lokacin da ake sa ran shugaban kasar Xi Jinping zai rattaba hannu kan wata yarjejeniyar sauyin yanayi da Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.