Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Sojojin Turkiyya da Syria za su fara sintiri kan iyakokinsu

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya ce ranar Juma’a hadin gwiwar dakarun kasar da na Syria, za su soma aikin sintirin tabbatar da tsaro a kan iyakar kasashen biyu a yankin arewacin Syria, wanda mayakan Kurdawa suka janye daga cikinsa.

Dakarun Kurdawa (YPG) a arewacin birnin Qamishli watan disambar, 2018.
Dakarun Kurdawa (YPG) a arewacin birnin Qamishli watan disambar, 2018. Delil SOULEIMAN / AFP
Talla

Shugaban na Turkiya ya bayyana haka ne a wannan laraba, lokacin da yake karin bayani a zauren majalisar kasar, dangane da halin da ake ciki a yankunan da mayakan Kurdawan na YPG suka janye, inda a karkashin wata yarjejeniya da suka cimma cikin makon jiya a birnin Sochi, Turkiya da Rasha ke shirin kafa katafaren yankin tsaro ko na tudun mun tsira, don tsugunar da ‘yan gudun hijirar Syria.

To Sai dai shugaba Erdogan ya yi gargadin cewa, dakarun Turkiya na da damar kai farmaki kan arewacin Syriar muddin ta gano akwai ragowar mayakan Kurdawan da suka ki janyewa, ko kuma suka kai wa sojin Turkiya hari.

A baya bayan nan hukumomin tsaron Rasha, suka ce adadin mayakan Kurdawan YPG da Turkiyya ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda sun kai dubu 34, tare da tarin makamansu daban daban dubu 3 da 260, daga sassan da ake shirin kafa yankin tsaron da nisan akalla kilomita 30 daga kan iyakar Syria da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.