Isa ga babban shafi
Rasha- Afrika

Za mu bunkasa cinikayya da Afrika- Putin

Shugaba Vladimir Putin da ke gabatar da jawabi a gaban shugabannin Afrika a birnin Sochi, ya ce, Rasha za ta ninka harkokin kasuwanci tsakaninta da nahiyar Afrika cikin shekaru biyar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin na gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen Afrika a birnin Sochi na Rasha
Shugaban Rasha Vladimir Putin na gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashen Afrika a birnin Sochi na Rasha Reuters
Talla

Shugaba Putin da ke karbar bakwancin taron na kwanaki biyu, ya ce, a halin yanzu, Rasha na fitar da kayayyakin abincin da kudinsu ya kai Dala biliyan 25 zuwa nahiyar Afrika, adadin da ya ce, ya zarce kudin makaman da suke fitarwa da ya kai Dala biliyan 15.

Shugaban ya ce, suna fatan habbaka wannan cinikayya da Afrika nan da shekaru hudu zuwa biyar masu zuwa.

Shugaban ya kara da cewa, alakar cinikayyar da ke tsakanin Rasha da Afrika a yanzu, bai wadatar ba, yana mai cewa, akwai kyawawan abokan hulda da ke da makoma ta gari a Afrikan.

A karon farko kenan da Rasha ke shirya irin wannan taro da ke samun halartar gomman shugabannin Afrika a daidai lokacin da kasar ke neman fadada tasirinta a nahiyar wadda kasashen Yammaci da China suka samu gindin zama a cikinta.

Sai dai a yayin zanta wa da Sashen Hausa na RFI, Alh. Isyaku Ibrahim, daya daga cikin tsoffin ‘yan siyasar Najeriya da ya zauna a Rasha, ya gargadi kasashen Afrika kan mayar da kansu mabarata a gaban manyan kasashen duniya.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hira da Alh. Isyaku Ibrahim.

03:00

Alh. Isyaku Ibrahim kan taron Rasha da Afrika

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.