Isa ga babban shafi
Birtaniya

An gano gawarwaki 39 makare a mota a Birtaniya

Jami’an ‘yan sandan Birtaniya sun ce, an gano gawarwakin mutane 39 makare a cikin wata motar kwantena wadda ta fito daga kasar Bulgaria.

Wurin da aka gano gawarwakin mutane 39 makare a cikin akwatin katuwar mota a Birtaniya
Wurin da aka gano gawarwakin mutane 39 makare a cikin akwatin katuwar mota a Birtaniya REUTERS
Talla

Jami’an ‘yan sandan Essex sun ce, an tabbatar da mutuwar daukacin mutanen a wurin da aka gano gawarwakinsu a gabashin birnin London, yayin da binciken farko ya nuna cewa, 38 daga cikinsu, manya ne, sai kuma matashi guda.

Tuni aka cafke direban motar mai shekaru 25 daga arewacin Ireland saboda zargin sa da aikata laifin kisan kai.

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya bayyana kaduwarsa da wannan al’amari, kuma tuni ya aika da sakon jaje ga iyalan mutanen.

Johnson ya ce, a halin yanzu, yana samun sabbin labarai akai-akai, yana mai cewa, Ma’aikatar Cikin Gida za ta yi aiki tare da jami’an ‘yan sandan Essex domin gano hakikanin abin da ya faru da mamatan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.