Jami'an tsaro sun kame daruruwan masu yada bidiyon batsa a kasashe 38
Hukumomin tsaron Birtaniya da Amurka, sun sanar da kame daruruwan ma’aikatan wani shafin Intanet mai cibiya a Korea ta Kudu, dake yada hotuna da bidiyon batsa, da ake lalata da kananan yara.
Wallafawa ranar:
An dai samu nasarar kamen ne, bayan kai samame a kasashe sama da 30.
Hadin gwiwar Jami’an tsaron, ya sanar da kame mutane 337 ne a kasashe 38, ciki har da Canada, Jamhuriyar Czech, Saudiya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, Spain, Jamus da Ireland, sai Amurka da Birtaniya, da kuma Korea ta Kudu inda cibiyar yada badalar take.
Hukumar yaki da laifuka ta Birtaniya, ta ce shafin yada badalar na dauke da bidiyon lalata da kananan yara da adadinsu ya kai kimanin dubu 250, wadanda akalla mutane miliyan guda a sassan duniya suka sauke a komfuta ko wayoyinsu na hannu.
Jami’an na Birtaniya sun kara da cewa, shafin yada badalar mai cibiya a Korea ta Kudu, na daga cikin ire-irensa na farko, da suka shahara wajen kasuwancin bidiyon cin zarafin kananan yara.
Ita kuwa ma’aikatar shari’ar Amurka bayyana shafin na Intanet din tayi a matsayin mafi muni a tsakanin takwarorinsa dake yada hotunan na lalata kananan yara.
A shekarar 2017 aka soma kame mutanen da ke tafiyar da wannan kafa, inda a Birtaniya aka zartas da hukuncin daurin shekaru 22 kan mutum na farko da aka kama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu