Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Farmakin Turkiya kan Kurdawa ya raba kan kasashen NATO

Rahotanni na nuni da cewa hare-haren Turkiya kan Kurdawa a arewacin Syria, sun haddasa rarrabuwar kai tsakanin kasashen kungiyar tsaro ta NATO.

Dakarun Sojin Turkiya a farmakin da su ke kaddamarwa a arewacin Syria.
Dakarun Sojin Turkiya a farmakin da su ke kaddamarwa a arewacin Syria. AFP/Delil Souleiman
Talla

Rarrabuwar kan ta fito fili ne, bayan da wasu kasashen kungiyar ta NATO suka yanke huldar saidawa Turkiyan makamai, a dalilin farmakin da dakarun kasar ke ci gaba da kai wa mayakan Kurdawa.

Har yanzu dai babu alamun Turkiya za ta amsa bukatar janye aniyar ta murkushe mayakan Kurdawan na YPG da ta ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda, duk da yanke huldar cinikin makamai da manyan kasashen Turai na Faransa da Jamus da Norway suka yi, da kuma takunkumin da Amurka ta laftawa karafan da Turkiyan ke shigarwa kasuwanninta.

Yayin jawabi a baya bayan nan, kan yakin na arewacin Syria, shugaban Turkiya Recep tayyib Erdogan ya yi watsi da duk wani tayin tattaunawa kan bukatar dakatar da hare-haren, inda ya shaidawa zauren majalisar kasar cewa, hanya daya tilo ta warware matsalar Syria, ita ce mayakan Kurdawa su mika makamansu, su kuma fice daga yankin tsaron da aka tsara ajiye ‘yan gudun hijira.

Sai dai duk da wannan alwashi, shugaban na Turkiya, ya ce zai gana da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da kuma sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, wadanda a yau suka tashi zuwa kasar ta Turkiya, domin tattaunawa da shugaba Erdogan kan yakin na arewacin Syria.

Yau ne kuma Faransa ta ce bincike ya nuna cewar, farmakin da Turkiya ke kaiwa arewacin Syrian, baya barazana ga gidajen Yarin da Kurdawa ke tsare da mayakan IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.