Isa ga babban shafi
Amurka

Kotu ta bukaci Trump ya gabatar da shaidar biyan haraji

Wani alkalin kotu a Amurka ya kalubalanci shugaban kasar Donald Trump kan ya gabatar da takaddunsu na shaidar biyan harajinsa na shekarun da suka gabata.

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Leah Millis
Talla

Matakin alkali Victor Marrero wanda ya gabatar da wani hukunci mai shafi 75 ya bayyana cewa, shugabannin basu da kariyar togewa daga tuhuma ko kuma bincike kan laifukan da suka shafi kaucewa biyan haraji.

Hujjojin alkali Victor Marrero dai na kalubalantar karar shugaba Donald Trump da ke neman janye tuhumar da ake masa game da kaucewa biyan harajin na tsawon shekaru.

A cewar Alkali Marrero kotun wadda ke a gundumar New York ba za ta iya mutunta bukatar shugaban ba, la’akari da hakan zai iya shafar tsarinta na tabbatar da adalci a hukuncin.

Matakin Kotun dai ya bude sabon shafi a tuhumar da Trump ke fuskanta wanda aka shafe tsawon lokaci ana bukatar ya gabatar da kwafin takardun shaidar biyan harajinsa.

Tuni dai lauyoyin da ke kare shugaba Trump suka daukaka kara kan batun wanda ya dakatar da umarnin waccan kotun na dan wani wa’adi kafin ci gaba da sauraron shari’a.

Tun farko dai alkalin gundumar Manhattan Vance Jr, ne ya shigar da karar da ke bukatar Donald Trump ya gabatar da takaddun shaidar biyan harajinsa daga bana zuwa shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.