Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Umar Sani kan ikirarin David Cameron game da matan Chibok

Wallafawa ranar:

Tsohon Firaministan Birtaniya David Cameron ya zargi tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kin amince wa da bukatar kasarsa ta ceto ‘Yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno. Wannan ikirarin da Cameron ya wallafa a  littafinsa mai take 'For The Record' ya haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen Najeriya, kuma tuni tsohon shugaban ya karyata zargin a sanarwar da fitar. Dangane da wannan cece-kuce, Bashir Ibrahim ya tattauna da Malam Umar Sani, mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo wanda ya ce, babu kamshin gaskiya kan zargin. Kuna iya latsa alamar hoton labarin don sauraren cikakken hirar.

David Cameron da Goodluck Jonathan
David Cameron da Goodluck Jonathan Getty Images
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.