Isa ga babban shafi
Amurka-Biden

Trump ya tafka kuskure kan neman Ukraine ta binciki Biden- Romney

Sanata Mitt Romney na jam’iyyar Republican wanda kuma ya yi kaurin suna sakamakon sukar lamirin shugaba Donald Trump na Amurka, ya ce babban kuskure ne kuma abin damuwa kiran da shugaban ya yi wa takwaransa na Ukraine don ya binciki Joe Biden.

Dan takarar neman shugabancin Amurka a shekarar 2020 Joe Biden
Dan takarar neman shugabancin Amurka a shekarar 2020 Joe Biden REUTERS/Scott Morgan
Talla

A cewar Mitt Romney a zahiri kiran da shugaba Donald Trump ya yi wa China da Ukraine don su bincike Joe Biden kuskure ne kuma abin assha’’ wadannan su ne kalaman dan majalisar dattawan na Amurka wanda ya taba neman jam’iyyar Republican ta tsayar da shi takara a zaben shugabancin kasa na 2012.

Romney ya ce idan har wani ba’amurke musamman ma wanda ke rike da mukamin shugaban kasa zai nemi China ta bincika masa wani da ke son tsaya wa jam’iyyar Democrat takara a zabe mai zuwa, to ba wani dalilin da zai sa ya nemi hakan face siyasa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani mai suna Kurt Volker, ya gabatar wa kwamitin da majalisar wakilai ta kafa don binciken wannan zargi da ake yi wa Trump da wasu jerin sakonnin SMS da aka yi musaya tsakanin manyan jami’an gwamnatin Ukraine dangane da wannan bukata ta Trump.

Ita dai Majalisar wakilan Amurka wadda ‘yan jam’iyyar Democrat ke da rinjaye, ta ce ba gudu ba ja da baya a game da wannan yunkuri na tsige shugaba Trump sakamakon wannan zargi da ake yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.