Isa ga babban shafi
MDD

Dole Trump da Rouhani su gana a Amurka- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, taron Majalisar Dinkin Duniya da ke gudana a birnin New York na Amurka, zai kasance wata 'hambararriyar dama' muddin shugaban Iran Hassan Rouhani ya gaza ganawa da Donald Trump.

Shugaban Amurka Donald Trump na Amurka da shugaban Iran Hassan Rohani
Shugaban Amurka Donald Trump na Amurka da shugaban Iran Hassan Rohani HO, NICHOLAS KAMM / AFP / IRANIAN PRESIDENCY
Talla

Shugaba Macron ya ce, muddin Rouhani ya koma Iran ba tare da ganawa da Trump ba, babu shakka an rasa wata dama ta musamman domin kuwa, ba lallai ba ne ya sake dawowa Amurka nan da wasu ‘yan watanni.

Macron ya kara da cewa, Trump ba zai ziyraci Tehran ba, a don haka ya zama dole shugabannin biyu su tattaunawa da juna a yanzu.

An dai yi zaton cewa, shugabnnin na kasashen Iran da Amurka masu hamayya da da juna za su yi wata ganawa ta musamman a daura da taron na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da Trump ke cewa, babu wani batun shirya zama a tsakanisa da takwaran nasa.

Shugaba Macron na ci gaba da jagorantar yunkurin shirya ganawa mai cike da tarihi tsakanin shugabannin biyu wadanda kasashensu suka shafe gomman shekaru suna nuna wa juna yatsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.