Turai ta zargi Iran da kai hari Saudiya
Shugabanin Kasashen Turai da suka hada da na Faransa da Jamus da kuma Birtaniya sun bayyana cewar Iran ce ta kai hari cibiyar samar da man Saudi Arabia, inda suka bukaci kasar ta dauki matakan diflomasiya domin warware matsalolin ta maimakon takalar fada.
Wallafawa ranar:
Shugaba Emmanuel Macron da Angela Merkel da Boris Johnson sun bayyana karara cewar ya zama wajibi Iran ta dauki alhakin kai harin a sanarwar hadin gwuiwa da suka bayar a Majalisar dinkin Duniya, inda suke cewa suna goyan bayan daukan matakan diflomasiya wajen magance matsalar.
Shugabannin sun kuma bukaci Iran ta koma mutunta yarjejeniyar nukiliyar da suka kulla a shekarar 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu