Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya jaddada akidar fifita Amurka a zauren MDD

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci takwarorinsa na kasashen duniya da su fiifta muradun kasashensu tare da kare kan iyakokinsu, yayin da ya ya yi tsokaci kan barazanar Iran.

Shugaba Donald Trump na Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Donald Trump na Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Lucas Jackson
Talla

A yayin gabatar da jawabinsa a zauren Majalisar Dinkin Duniya a wannan Talata, shugaba Trump ya nanata cewa, masu akidar fifita kasashensu ne kawai za su samu makoma ta gari.

Shugaban ya ce, tsaron Amurka na cikin wani hali na fargaba saboda barazanar da ke kunno kai daga Iran, yayin da ya gargadi mahukuntan Trhran da su daina takalar kasashe aminan Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya ce, muddin Iran ta ci gaba da nuna mummunar dabi’a, babu shakka ba za a janye takunkuman da aka kakaba mata ba, sai dai ma a sake tamke su.

Kodayake Mr. Trump ya ce, Amurka ba ta neman tashin hankali da kowacce kasa, yana mai cewa, suna kaunar zaman lafiya da hadin kai.

Jawabin Trump a zauren na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da ‘ya’yan jam’iyyar Democrat ke ci gaba da matsa kaimi don ganin an tsige shi daga karagar mulki bayan fallasar wasu bayanai da ke nuna cewa, shugaban ya bai wa wani jami’insa umarnin biyan Ukrain tallafin Dala miliyan 400.

Bayar da tallafin na zuwa ne kwanaki kalilan gabanin wata zantawa ta wayar tarho da ya yi da shugaban kasar ta Ukraine, inda ya bukace shi da ya gudanar da bincike kan iyalan Joe Biden, tsohon mataimakin shugaban Amurka wanda ya kasance daya daga cikin jiga-jigan masu adawa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.