Isa ga babban shafi

Trump zai ladabtar da Iran kan harin Saudiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya na da matakai da dama da zai iya dauka a matsayin martini kan Iran cikinsu harda kai harin soji, yayin da ake saran bayyana sabbin takunkumin da ya dorawa kasar cikin sa’oi 48 masu zuwa.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Yayin da manema labarai suka tambaye shi ko akwai yiwuwar kaiwa Iran hari, shugaabn ya ce akwai hanyoyi da dama da suka hada da manya da kuma kanana, yayin da babbar hanyar ita ce yaki.

Saudi Arabia da ke matsayin babbar kawar Amurka ta ce babu tantama Iran ce ta dauki nauyin kai hari kan cibiyoyin tace man ta a makon jiya.

Tun bayan farmakin wanda ya kassara cibiyoyin man na Saudiya tare da haddasa tsadarsa a kasuwar duniya, Iran ta musanta hannu a harin wanda 'yan tawayen Houthi suka dauki alhakinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.