Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Adadin bakin - haure a duniya ya kai miliyan 272

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin bakin – haure a duniya yanzu ya kai miliyan 272, kuma nahiyoyin Turai da Arewacin Amurka ne ke dauke da mafi yawan wadannan mutane, wadanda yawan su ya karu da kashi 23 a shekaru goma da suka wuce.

António Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya
António Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Rahoton ya gano cewa akwai bakin – haure miliyan 82 da ke zaune a nahiyar Turai, da miliyan 59 a nahiyar Arewacin Amurka a shekarar 2019, sai kuma miliyan 49 a nahiyar Asiya.

Yawan bakin - haure a duniya a shekarar 2019 ya zarce yadda yake a shekarar 2010 da mutane miliyan 51, wato kari na kashi 23 kenan a cewar rahoton na hukumar kula da yawan al’umma ta majalisar Dinkin Duniya.

An yi amannar cewa, kashi 3.5 na yawan al’ummar duniya a yanzu bakin – haure ne, idan aka kwatanta da kashi 2.8 a shekarar 2000.

Rahoton ya ce wannan kiyasin an samo shi ne daga kididdiga ta hukuma daga kidayar jama’a da kasashe suka gudanar.

‘’Wadanan bayanai suna da matukar amfani wajen fahimtar mahimmancin bakin – haure da ma yin balaguro ga ci gaban kasashen da suke zuwa da kasashen su na asali’’ a cewar Liu Zhenmin, sakateren hukumar tattalin arziki da abin daya shafi zamantakewa.

Ya ce yin balaguro ta hanyar da ta dace yana da mahimmanci ga ci gaba mai dorewa.

Nazarin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na kasa bayan kasa, na nuni da cewa, rabin wannan adadi na bakin – haure miliyan 272 na zaune ne a kasashe 10, in da Amurka kawai ke da miliyan 51.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.