Merkel ta damu dangane da rikicin kasuwancin China da Amurka
Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce, rikicin kasuwancin Amuka da China na shafar duniya baki daya, yayinda ta bayyana fatan magance wannan matsalar a kan lokaci.
Wallafawa ranar:
Uwargida Merkel ta bayyana haka ne a yayin bude zaman tattaunawarta da Firimiyan China, Li Keqiang a birnin Beijing, inda take ziyarar kwanaki biyu.
Mista Li Mai shekaru 63 da haihuwa, Kwararre ne a fannin tattalin arziki,ganawar na a matsayin sako zuwa yan kasuwa da cewa Jamus ta damu ainu da halin da manyan kasashen Amurka da China suka fada a yau.
A cewar Uwargida Angela Merkel tabbas lamarin na daf da kawo rudani ga harakokin cinikaya da kasuwancin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu